Spurs na harin Tonali, Madrid na son Dias
An na kara karfafawa Tottenham guiwa wajen siyen Sandro Tonali, Real Madrid na harin Ruben Dias, yayin da Manchester Unitedta tsayar da farashi kan Marcus Rashford valuation.
An ƙarafafawa Tottenham guiwa wajen gogayya da Arsenal da Manchester City siyen ɗan wasan Italiya Sandro Tonali, inda Newcastle ke neman fam miliyan ɗari kan ɗan wasan. (Telegraph - subscription required)
Real Madrid na harin ɗan wasan Manchester City Ruben Dias. (Mirror)
Manchester United sun yi wa Marcus Rashford farashin fam miliyan 40, sai dai an fidda ran komawar ɗan wasan Liverpool ko Manchester City. (ESPN)
Manchester United na son ƴan wasan West Ham Mateus Fernandes da Crysencio Summerville sai dai West Ham din na son a basu fam miliyan ɗari da arba'in da ɗan wasan tsakiyar Portugal Fernandes, da ɗan wasan Netherlands Summerville, (Mail)
Arsenal sun amince da sharuɗan ɗan wasan Faransa Manu Kone, sai dai ba su kai ga tsayar da magana da Roma kan farashi ba, inda suke neman Euro miliyan 50 dai-dai da fam miliyan 43.2. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Liverpool na ci gaba da ƙoƙarin ta na ɗauko ɗan wasan Yan Diomande RB Leipzig, inda sabon mai horar da ƴan wasan Andoni Iraola, ya amince da ɗauko ɗan wasan. (Teamtalk)
Mancester City da Chelsea sun fara tuntuɓar wakilan Marco Palestra, sai dai basu fara tattaunawa ba da ɗan wasan na Atalanta ba. (Sky Sport Italia - in Italian)
Al-Hilal sun sake sabunta yunƙurinsu na ɗaukar dan wasan Barcelona Raphinha, sai dai dan wasan bayan son ya tattauna makomar sa har sai bayan gasar cin kofin duniya da ake. (Globo - in Portuguese)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Everton na dubar yauwuwar ɗaukar ɗan wasan Belgium Lois Openda da ke matsayin ɗan wasan aro a Juventus. (Football Insider)
Leeds da Notthingham Forst sun shiga sahun masu zawarcin Openda (Teamtalk)
Marseille ta shirya sake tattaunawa da ɗan wasan Ingila Angel Gomes, yayin da Coventry da Hull ke neman ɗan wasan, inda ya kamala zamansa a matsayin ɗan wasan aro a Wolves a kakar da ta gabata. (Teamtalk)
Inter Mila ta zama ƙungiya ta farko a baya-bayan nan, da ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan Faransa Eduardo Camavinga, daga Real Madrid a wannan kaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Brighton na jan ƙafa wajen biyan fam miliyan 60 ga ɗan wasan Tottenham da Croatia Luka Vuskovic, wanda a kakar wasan da ta gabata ke matsayin ɗan wasan aro a Hamburg. (Football Insider)
Tottenham ta ƙi amincewa da masu taya ɗan wasan Ingila Will Kankshear, inda Tottenham ɗin ke son fam miliyan 20 kan ɗan wasan, da ke ƙawazo a taka ledar da yake yi a matsayin ɗan wasan aro a Oxford a kakar bara, inda Sporting ke sa ido a kansa. (Hayters)
Paris FC ta tuntubi tsohon mai horar da ƴan wasan Chelsea Liam Rosenior kan yiwuwar maye gurbin A
📌 Kaynak
Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →