Yadda majalisar wakilan Najeriya ta samar da kudurori don inganta tsaro

📌 Diğer 📰 Nigeria 🕐 3 saat önce
Yadda majalisar wakilan Najeriya ta samar da kudurori don inganta tsaro

Majalisar wakilan Najeriya ta kammala sauraron ra'ayin jama'a akan wasu kudurorin don inganta tsaro

Majalisar Wakilan Najeriya ta kammala sauraren jin ra'ayin jama'a kan jerin wasu kudirori da suka shafi inganta tsarin aikin soji da kyautata jin dadinsu da kuma karfafa masu tunkarar duk wata barazana.

Hon. Ahmad Abdullahi Kalambaina, dan majalisar wakilai ne daga jihar Sokoto, kuma mataimakin shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilan Najeriyar, ya shaida wa BBC cewa kudurorin da aka gabatarwa majalisar sun shafi yin sashe na hadaka tsakanin sojojin Najeriya don a samu ci gaba, sai kuma kudurin samar da babbar kwalejin ilimi ta sojoji da kuma kudirin yadda za a samar da wata kafa ta kulawa da tsoffin sojoji idan sun yi ritaya.

Ya ce," Batun dawowa da yadda za a rinka kulawa da tsoffin soji, dama tun a shekarun bayan ana yin hakan, to shi ne ake so a dawo da kudurin don ayi masa gyara ta yadda za a rinka kulawa da ainihin wadanda suka yi wa Najeriya hidima koda kuwa ba sa raye za a kula da iyalansu."

Dan Majalisar tarayyar, ya ce," Kuma ko shakka babu wadannan kudurori za su taimaka wajen inganta tsaro musamman a wannan yanayi da ake ciki."

" Yanzu mataki na gaba da zamu dauka shi ne tun da mun gama jin ra'ayin jama'a akan kudurorin, zamu je mu zauna mu rubuta rahoto mu mikawa majalisa, daga nan idan aka duba rahoton sai kuma a aje majalisar dattijai nan ma a samu fahimta akan kudurorin tsakaninmu da su, daga nan kuma sai ya zama doka idan an sanya hannu."

A Najeriya dai ana ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda hare-haren 'yan fashin daji suka zama ruwan dare a wasu jihohi.

Jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da ke makwabtaka da juna na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar irin waɗannan hare-hare, inda maharan ke kai farmaki kan ƙauyuka da garuruwa, tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

A wasu lokutan kuma, maharan kan farmaki manoma a gonakinsu ko matafiya a kan manyan hanyoyi, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da haddasa fargaba a tsakanin al'umma.

Matsalar ta yi tasiri sosai kan harkokin noma da kasuwanci, musamman a yankunan karkara da ke dogaro da noma a matsayin babbar hanyar samun abin rayuwa. A lokuta da dama, manoma kan kasa zuwa gonakinsu saboda tsoron hare-hare, abin da ke haifar da fargabar ƙarancin amfanin gona da kuma ƙarin matsin tattalin arziki ga mazauna yankunan.

Duk da cewa gwamnati da jami'an tsaro sun sha ƙaddamar da hare-hare kan maboyar 'yan bindigar tare da tura ƙarin jami'ai zuwa yankunan da abin ya fi kamari, hare-haren na ci gaba da faruwa a wasu wurare.

Masana harkokin tsaro na ganin cew

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön