Gasar kofin duniya 2026: Abin da kuke son sani kan wasan Ingila da Croatia

📰 Gündem 📰 Nigeria 🕐 3 saat önce
Gasar kofin duniya 2026: Abin da kuke son sani kan wasan Ingila da Croatia

Wannan shafin zai ke kawo muku yadda take kayawa tsakanin Ingila da Croatia har da hasashe da ƙididdigar karawar

Manyan tawagar nahiyar Turai biyu za su kara tsakanin Ingila da Croatia a gasar cin kofin duniya wasan farko a rukuni na 12 da za su kece raini a Dallas

Croata, wadda ta ƙare a mataki na uku a Qatar a 2022, ita ce ta yi rashin nasara a hannun Faransa a wasan ƙarshe a 2018, wadda ta kammala wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta 2026 ba tare da rashin nasara ba a karawar cikin rukuni.

Ita kuwa Ingila ƙarƙashin sabon kociya, Thomas Tuchel ta samu gurbin shiga wasannin da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico da lashe dukkan wasannin cikin rukuni.

Ingila za ta fara ƙoƙarin kawo ƙarshen shekaru 60 ba tare da lashe Kofin Duniya ba a ranar Laraba, yayin da za ta fafata da Croatia a wasan farko a rukuni na 12 da za su kece raini a Arlington a birnin Texas.

Kocin Ingila ɗan Jamus, Thomas Tuchel, ya bayar da mamaki ga mutane da dama lokacin da ya fitar da jerin ƴan wasa 26 da za su wakilcin Ingila a gasar cin kofin duniya a 2026, amma ba su haɗa da fitattun taurari irin su Phil Foden na Manchester City da Cole Palmer na Chelsea da Harry Maguire na Manchester United da kuma Trent Alexander-Arnold mai taka leda a Real Madrid ba.

Sai dai duk da wannan, yana da wuya a yi shakku kan wannan hukuncinsa, ganin cewa ya jagoranci Ingila a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da lashe dukkan wasa takwas ba rare da an doke shi ba.

Tsohon ɗan wasa, Jordan Henderson, wanda zai cika shekaru 36 a ranar wasan, yana daga cikin masu goyon bayan wannan tsarin da Tuchel ya ɗauka, yana ganin zai taimaka wajen gina matasa da haɗin kai mai ƙarfi a cikin tawagar.

Duk da haka, Henderson ya yarda cewa wasan nan ba zai zowa Ingila cikin sauki ba, kamar yadda suka samu a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya, musamman idan aka yi la'akari da ƙwarewar Croatia da fitattun ƴanwasanta da tarihin ta a manyan gasa.

Croatia ta shiga gasar Kofin Duniya ta bana da fatan ci gaba da salon da ya sa aka san ta a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke yin fiye da abin da ake tsammani a kowacce gasar a ƙwallon ƙafa.

Sai dai shirye-shiryenta sun ɗan samu cikas, saboda raunin kyaftin ɗinta, Luka Modrić, wanda ke da shekara 40. Likitoci sun yi masa tiyata a watan Afrilu, amma ana sa ran zai warke ya dawo taka leda, ya kuma jagoranci kasarsa a wannan babbar gasar tamaula ta duniya.

Modrić har yanzu shi ne zuciyar tawaga Croatia, kuma wannan gasar za ta samar da damar da kasar za ta cakuɗa tsaffi da sabbin jini a fannin taka leda a tawagar Croatia.

Modrić, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a 2018, da ɗaukar manyan kofuna 28 tare da Real Madrid, zai buga gasar ta Kofin Duniya

#war

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön