Abubuwan da muka sani kan yarjejeniyar Iran da Amurka
Har yanzu dai ƙasashen biyu ba su fitar da wata takarda da ta ƙushi yarjejeniyar a hukumance ba, amma sun ambaci wasu sharuɗɗan da ke ƙunshe a cikin ta.
Bayan da aka sanar cewa Iran da Amurka sun cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna, kamfanin dillancin labarai na Mehr ya wallafa wasu sabbin bayanai kan daftarin yarjejeniyar fahimtar juna mai kunshe da sharuɗɗa 14, inda ya ambato wata majiya da ke kusa da tawagar Iran ɗin.
Wannan taƙaitaccen rubutun yana jaddada mahimman buƙatu da yawa a cikin sakin layi na farko: kawo ƙarshen yaƙi a kowane fage, gami da Lebanon; cikakken ɗage shingen cikin teku; buɗe mashigar Hormuz a cikin kwanaki 30; da kuma dakatar da takunkumin sayar da mai. Iran ta kuma jaddada aniyar ta na kin ƙera makaman nukiliya.
Ɗaya daga cikin sharuɗɗan ya kuma ƙunshi cewa, dole ne a saki dala biliyan 24 na kadarorin Iran da aka daskarar a cikin kwanaki 60, a daidai lokacin da aka kammala tattaunawar, tare da bai wa Iran rabin kuɗaɗen kafin a fara tattaunawar.
An kuma wallafa wata maƙala a cikin harshen Larabci a kafafen yaɗa labarai na Larabawa wanda kusan ya yi kama da na kamfanin dillancin labarai na Mehr, amma ba a taƙaita ko rarraba shi ba, inda aka yi shi a matsayin cikakkiyar maƙala.
Sai dai gidan talabijin na Channel 12 na Isra'ila ya wallafa taƙaitaccen bayani mai ɗauke da abubuwa 12 da suka yi kama da na kamfanin dillancin labarai na Mehr, inda babban abin da ya bambanta shi ne cewa ba a ambaci adadin "dala biliyan 24" ba dangane da sakin kadarorin Iran da aka daskarar.
Sa'a guda bayan wallafa wannan rubutu a kamfanin dillancin labarai na Mehr, Donald Trump ya mayar da martani a kan sa cikin fushi, inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: "Sharuɗɗan da Iran ta bayana wa ƙafafen yaɗa labaran ƙarya ba su da alaƙa da sharuɗɗan da aka amince da su a rubuce. Abin da suka faɗa ciki har da maganar shiriritar da suka yi game da tabbacin cimma yarjejeniya, ba shi da wata alaƙa da gaskiya. Ba su da wani aminci a wurin tattaunawa, ba su san abin da ake kira tattaunawa cikin aminci ba. Abin mamaki."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Kafar yaɗa labarai na intenet ta Tabnak ta wallafa wani rubutu mai taken "Cikakken bayani na yarjejeniyar fahimtar juna, wanda aka ce shi ne na ƙarshe."
Wannan rubutun yana da bambance-bambance masu mahimmanci da dama daga na kamfanin dillancin labarai na Mehr, kuma bai ambaci adadin "dala biliyan 24" ba kuma kawai ya ambaci sakin daskararun kadarori ne. Bugu da ƙari, rubutun da kamfanin dillancin labarai na Mehr ya wallafa ya bayyana cewa, "dole ne a ba da rabin wannan adadin ga Iran kafin a fara tattaunawa," yayin da rubutun Tabnak ya bayyana cewa, za a saki kadarorin da aka daskarar "a yayin da ake ci gaba da tattaunawa
📌 Kaynak
Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →