Abin da masana ke cewa kan wajabtawa 'yan takara NDC yin rantsuwar zama a jam'iyyar bayan cin zaɓe

📰 Gündem 📰 Nigeria 🕐 4 saat önce
Abin da masana ke cewa kan wajabtawa 'yan takara NDC yin rantsuwar zama a jam'iyyar bayan cin zaɓe

Yadda masana ke kallon matakin jam'iyyar NDC na wajabtawa 'yan takara yin rantsuwa akan ba za su fice daga jam'iyyar ba bayan sun ci zabe

Masu sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya, sun fara tsokaci akan matakin da jam'iyyar NDC ta bullo da shi na wajabta wa yan takararta a matakai daban-daban yin rantsuwa a rubuce akan idan suka ci zabe ba za su fice daga jam'iyyar ba.

Jam'iyyar ta ce dukkan 'yan takararta ciki har da Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sai sun yi alƙawarin cewa za su bar musu kujerunsu idan suka sauya sheka daga jam'iyyar bayan sun ci zaɓe.

Masanan irinsu Farfesa Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa, wannan mataki da jam'iyyar ta ADC ta dauka, mataki ne na ba sabonba, sannan za a iya cewa an dauki matakin da kyakkyawar niyya ta hana wani abu da mutane ke ganin ba daidai bane ba.

Ya ce," Yanzu abin da ke faruwa shi ne mutane sun mayar da jam'iyyu kamar motar da zata kai ka wani waje inda ta sauke ka sai ka tafi ka barta."

"To amma a wani bangare kuma, ina ganin wannan matakin ba lallai bane ya samu nasara, tun da a yanzu dokoki daban daban har ma da dokar zabe ta kasa dama tsarin mulkin Najeriya bai yarda da wani nau'i na canja sheka da ake yi ba, abin da tsarin mulkin ya yarda dashi ne wadanda ke a bangaren zartarwa ne kadai za su iya sauya sheka." In ji shi.

Ya ce," Su kuwa bangaren majalisar za su iya sauya sheka ne idan jam'iyya ta dare biyu, to amma a halin da ake ciki yanzu a Najeriya, duk an yi watsi da abin doka da tsarin Mulki suka tanada, kowa na yin abin da ya ga dama."

Farfsesa Kari, ya ce," Ina ganin cewa bisa la'akari da abubuwan da ke faruwa yanzu a Najeriya, 'yan siyasa ba ruwansu da wata rantsuwa, don haka bana ganin wannan mataki na jam'iyyar NDC, zai yi tasiri."

"Domin sun sha yin rantsuwa a matakai daban-daban amma kuma sai su karya alkawari ko kuma su rinka abubuwan da za su karya rantsuwar da suka yi." In ji shi.

Ya ce," Matakin zai daure wasu ne, wasu kuma su shiga taitayinsu, sannan kuma ba lallai ba ne haka ta cimma ruwa."

Masanin siyasar, ya ce," Batun sauya shekar nan da 'yan siyasa ke yi yana illoli da dama, na farko karan tsaye ne ga doka, na biyu yana rage duk wani fata da ake da shi na cewa za ayi siyasar Akida, sannan na uku sauya shekar nan babban Rashin adalci ne ga wadanda suka zabi masu sauya shekar, don haka dukkan wadannan abubuwan nakasu ne ga tafarkin dimokradiyya."

#war

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön