Yadda kotu ta wanke Diezani daga laifukan rashawa

📌 Diğer 📰 Nigeria 🕐 3 saat önce
Yadda kotu ta wanke Diezani daga laifukan rashawa

An zargi Diezani, mai shekaru 65, da karɓar cin hanci daga attajiran masu harkar mai, ciki har da kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan biyu daga shahararren kantin Harrods, da rayuwa a gidaje masu tsada da kuma wasu alfarma a Birtaniya.

Wata kotu da ke birnin London ta wanke tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi mata bayan shafe shekaru ana gudanar da bincike da shari'a kan lamarin.

An wanke ta daga zargin karɓar cin hanci daga attajiran masu harkar mai ta hanyar zama a gidaje na alfarma da kuma bushasha da kuɗaɗe masu yawa a Birtaniya.

Hakan ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan shari'un da Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA) ta shafe sama da shekara goma tana bi, kuma aka wanke ta daga zarge-zarge biyar da ake mata.

Masu gabatar da ƙara sun zargi Diezani, mai shekaru 65, da karɓar cin hanci daga attajiran masu harkar mai, ciki har da kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan biyu daga shahararren kantin Harrods, da rayuwa a gidaje masu tsada da kuma wasu alfarma a Birtaniya.

An fara binciken Diezani ne a shekarar 2013, yayin da aka kama ta a London a shekarar 2015.

A lokacin tana daga cikin manyan jami'an gwamnatin Najeriya da suka yi fice a harkar mai, inda ta riƙe muƙamin minista tsakanin 2010 da 2015. Haka kuma ita ce mace ta farko da ta jagoranci ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.

Dama dai tun a farkon shari'ar a watan Janairu, lauyoyinta sun yi ta jaddada cewa akwai muhimman takardun da za su iya tabbatar da ba ta da laifi da suka ɓace a Najeriya. Sun kuma yi suka kan tsawon lokacin da aka ɗauka kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

Kotun ta kuma wanke ɗan'uwanta, Doye Agama, mai shekaru 69 kuma babban limamin wata cocin Pentecostal a Manchester, daga zargin haɗa baki wajen aikata rashawa, da kuma wani attajira a harkar mai, Olatimbo Ayinde mai shekaru 54.

A yayin shari'ar da ta ɗauki hankalin jama'a a birnin London, , Diezani ta yi ta ƙoƙarin kare kanta daga zarge-zargen rashawa ta hanyar bayyana kanta a matsayin mace mai bin doka da oda da kuma mai yaƙi da cin hanci da rashawa, inda ta ce tsananin bin ƙa'idojin aiki ne ya sa aka yi mata laƙabi da "Madam Due Process".

Diezani, wadda aka fi sani da "Madam D", ta shafe kwanaki goma tana bayar da shaida a gaban kotu, yayin da masu kallo suka riƙa cika ɗakin sauraron shari'ar, ciki har da baƙi daga Najeriya.

Kafin shigarta siyasa, Diezani ta samu gagarumin ci gaba a harkar gudanar da kamfanonin mai, inda a shekarar 2006 ta zama mace ta farko da aka naɗa cikin kwamitin gudanarwa na kamfanin mai da gas na Shell a Najeriya.

Da take bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta, Diezani ta shaida wa kotu cewa kasancewarta mace a irin wannan babban matsayi a fannin da mafi yawa maza ne ya jawo mata tsana daga wasu m

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön