Ko Iran ta yi nasara a yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka?
Ga Iraniyawa da dama, tambayar ba ita ce ko yarjejeniyar ta yi kama da nasara ba, amma abin la’akari shi ne ko ta yi sanadiyyar rage farashin kaya kuma ko ta rage fargabar sake ɓarkewar wani yaƙin.
Shugabanin Iran na ƙoƙarin gabatar da yarjejeniyar fahimtar juna da ta ƙulla da Amurka, a matsayin wata gagarumar nasara ba miƙa wuya ba. Amma wannan ba abu ne da zo musu da sauƙi ba..
A yanzu dai ƙasar ta na ƙoƙarin farfaɗowa daga mummunan yaƙi da ya yi ma ta matuƙar ɓarna yayin da tattalin arzikin ƙasar ke fuskantar matsananciyar matsin lamba, kuma wani ɓangaren masu goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kwashe tsawon watanni suna yin Allah wadai da duk wani matakin sasantawa da Washington.
Haka kuma akwai ƴan ƙasar Iran a ciki da wajen ƙasar, waɗanda ke ganin rikicin matsayin wata dama ce ta sauya gwamnatin ba wai lokaci na diflomasiyya ba.
Wannan shi ne rabe-raben siyasar da gwamnatin ke fuskanta kuma a cikin wannan halin ta ke neman ta tallata yarjejeniyar.
Manyan jami'an Iran na tallata yarjejeniyar a matsayin nasara. Mohammad Bagher Qalibaf, shugaban majalisar dokokin ƙasar Iran kuma jigo a tattaunawar, ya ce Iran ta ɗauki dogon lokaci zuwa kai wa ga nasara ta ƙarshe.
Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana yarjejeniyar da cewa za ta iya kawo sauyi, yana mai cewa idan har aka aiwatar da ita yadda ya kamata za ta iya magance yawancin matsalolin da Iran ke fuskanta da kuma haifar da wani yanayi na daban a Iran da kuma yankin gabas ta tsakiya baki ɗaya.
Matsayin Qalibaf yana da mahimmanci saboda ba a san shi da kasancewa mai matsakaicin ra'ayi irin na Pezeshkian ba; Goyon bayan da ya nuna wa yarjejeniyar a bainar jama'a ya nuna cewa yarjejeniyar tana samun goyon baya daga ɓangarorin gwamnati da ake yi wa ganin masu tsaurin ra'ayi, har ma daga cikin rundunar kare juyin juya halin Musulunci na Jamhuriyar Musuluncin.
Shugabannin suna kuma neman gabatar da yarjejeniyar a matsayin nasara domin a cewar Tehran, Amurka da Isra'ila sun gaza cimma manyan manufofinsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Ba su tilastawa Iran miƙa wuya ba, ba su kawar da Jamhuriyar Musulunci daga kan karagar mulki ba, ba su kawo ƙarshen shirin nukiliyar Iran ta hanyar soja ba, ba su kuma wargaza alaƙar Iran da Hezbollah ba.
A madadin haka, har yanzu Iran tana kan teburin tattaunawa, tare da shigar da Lebanon cikin tsarin ana kuma tatauna batun sassauta takunkumai.
An bayar da rahoton cewa, wani ɗan majalisar mai rajin ra'ayin riƙau, mataimakin shugaban kwamitin tsaron ƙasa, ya bayyana daftarin yarjejeniyar a matsayin wata takarda da za ta mayar da Iran ta zama ƙarƙashin mulkin Amurka.
Ya kuma zargi masu shiga tsakani da yin watsi da umarnin jagoran addinin ƙasar na kada a sake buɗe mashigar Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwan dakon kaya
📌 Kaynak
Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →