Gasar cin kofin duniya 2026: Kovacs ne zai busa wasa na 1,000 a gasar kofin duniya
Wannan shafin zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan gasar cin kofin duniya 2026 da sauran labaran wasanni a irin wannan lokacin
Tawagar Ivory Coast ta ci karo da koma baya gabanin muhimmin wasan da za ta kara da Jamus a gasar Kofin Duniya, bayan da aka tabbatar cewa ɗan wasanta, Elye Wahi ba zai samu shiga Kanada ba, tare da tawagar.
Hukumar Kwallon Ƙafa ta Ivory Coast (FIF) ta sanar a ranar Alhamis cewa har yanzu ba a kammala samun izinin shiga Kanada da ake buƙata ga ɗan wasan ba, saboda haka zai ci gaba da zama a Amurka har sai tawagar ta kammala karawar ta koma masauki.
Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da aka aka saka sunan Wahi kan wani bincike da hukumomin Faransa ke yi kan zargin almundahanar wasanni. Rahotanni ya nuna cewa an gano wasu abubuwan da suka shafi caca da kuma gargadinsa da aka taba yi a wani wasan Ligue 1 yayin da yake taka leda a Nice a watan da ya gabata.
Sai dai hukumomin Faransa ba su bayyana Wahi a matsayin wanda ake zargi ba. Wani kakakin ofishin masu gabatar da ƙara a Marseille ya shaida wa Reuters cewa an tsare wani ɗan wasan Ligue 1 mai shekara 23 a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin wani ɓangare na binciken da ake yi kan zargin damfara da cin hanci a harkar wasanni, karɓar kayan sata da kuma halasta kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Duk da haka, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Ivory Coast ta bayyana cikakken goyon bayanta ga ɗan wasan.
Wahi, wanda a baya ya wakilci Faransa a matakin ƴan ƙasa da shekara 21, ya fara buga wa Ivory Coast wasa a matakin manya ne a watan Maris.
Ivory Coast ta fara gasar bana da nasara bayan da ta doke Ecuador da ci 1-0 a wasanta na farko na rukuni na biyar, kuma Wahi ya buga fafatawar. Ita kuwa Jamus ta shiga wannan karawa cikin kwarin gwiwa bayan da ta lallasa Curacao da ci 7-1 a wasan farko.
Rashin Wahi na iya zama babban gibi ga Ivory Coast, musamman a wasan da za ta kara da ɗaya daga cikin ƙasashen da ake ganin za su iya lashe kofin duniya na bana.
📌 Kaynak
Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →