Yadda ƴan Najeriya suka fi ƴan kowace ƙasa ta duniya yin sadaka

📌 Diğer 📰 Nigeria 🕐 3 saat önce
Yadda ƴan Najeriya suka fi ƴan kowace ƙasa ta duniya yin sadaka

Shida daga cikin ƙasashe 10 na duniya da mutanensu suka fi taimaka wa juna sun fito ne daga Afirka, kuma Najeriya ce ta ciri tuta.

Rahoton wani nazari da gidauniyar bayar da sadaka ta Charity Aid Foundation ta fitar kan ƙasashen duniya da suka fi yin kyauta a shekara ta 2025, ya nuna cewa 6 daga cikin ƙasashe 10 da suka fi bayar da sadaka a duniya daga nahiyar Afirka suke.

Rahoton ya ce mutane a nahiyar Afirka na bayar da sadakar gwargwadon kashi 1.6% na abin da suke samu, yayin da a nahiyar Turai mutane ke bayar da kashi 0.6% na abin da suke samu a matsayin sadaka.

An gudanar da nazarin ne kan sama da mutum 500,000 a ƙasashe 101 na duniya.

Rahoton ya ce yanzu ana tantance girmar sadaka ne ba ta hanyar yawan mutanen da ke bayar da sadaka a ƙasa kawai ba, amma ana la'akari ne da yawan kuɗin da mutum ke bayarwa sadaka idan aka kwatanta da abin da yake samu, wanda ya bayar ga mabuƙata ko kuma domin ayyukan addini.

Ga ƙasashe 10 da suka fi bayar da sadaka da kuma dalilan da suka sanya suke a kan gaba.

Kashi 89% na ƴan Najeriya ne suka bayar da sadaka a shekarar 2024 - wanda wannan ne mafi yawa tsakanin ƙasashe 101 da aka yi nazari - wanda hakan ya sanya Najeriya ta zamo ta ɗaya a duniya cikin ƙasashen da mutanensu suka fi bayar da sadaka.

Nazarin ya kuma ce ƴan Najeriya na sadaukar da gwargwadon awa 13.5 wajen yin aikin hidimta wa al'umma a shekara, wanda hakan ya zarce gwargwadon yadda mutanen wasu ƙasashen ke sadaukar da lokutansu, gwargwadon awa 9.

Rahoton ya alaƙanta wannan sadaukarwa ta ƴan Najeriya ga tanade-tanaden addini, inda yan Najeriya masu ibada ke bayar da baiko a majami'u, sannan Musulmai ke bayar da zakka, wanda hakan ya zama wani ɓangare na rayuwarsu.

Sai dai ƴan Najeriya da dama na ganin cewa za su iya zuwa a matsayi na 22 cikin jerin ƙasashen da mutanensu suka fi bayar da sadaka, wanda hakan ke nuna yadda ɗabi'ar bayar da sadaka ta zamo jiki a gare su.

Masar ce ƙasa ta biyu a duniya wajen bayar da sadaka, sanadiyyar yadda mutanenta suka aminta da ƙungiyoyin bayar da taimako.

Ƙarfin amincin da al'umma ke da shi da irin waɗannan ƙungiyoyi ne ya sanya mutane ke yawan ba da gudumawa, wani abu da ke da matuƙar tasiri a ƙasashe da dama da aka yi nazari a kai.

Ghana na cikin ƙasashen da al'ummarta suka fi bayar da taimako a Afirka, musamman kai-tsaye ga mabuƙata da kuma domin ayyukan addini.

Ita ce wata ƙasa da ba ta Afirka ba da take cikin ƙasashen da suka fi bayar da tallafi a duniya.

Hakan ya nuna cewa ba ƙasashe marasa ƙarfi ne kawai ba ake da yawan masu bayar da taimako ba.

Sai dai rahoton ya ce mutane a ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na bayar da taimako, amma idan aka yi la'akari da abin da suke bayarwa gwargwadon abin da suke samu, hakan ya yi ƙasa

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön