Iran ta ce ta kai hare-hare 85 kan sansanonin sojin Amurka

📌 Diğer 📰 Nigeria 🕐 1 saat önce
Iran ta ce ta kai hare-hare 85 kan sansanonin sojin Amurka

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa game da jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/07/2026

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ƙaru da sama da kashi biyar cikin 100 ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe.

Bayan kalaman Trump, farashin ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin kasuwar mai ta duniya, ya tashi zuwa dala 78.09 kan kowace ganga.

Rahotanni sun nuna cewa masu zuba jari na sa ido sosai kan yadda rikicin tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara taɓarɓarewa.

Tun kafin wannan sanarwa, farashin mai ya fara nuna alamun tashin gwauron zabi sakamakon musayar hare-haren da Amurka da Iran suka yi wa juna, musamman bayan hare-haren da aka kai kan tankokin dakon mai a mashigar Hormuz.

Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa idan rikicin ya ci gaba da tsananta, hakan na iya ƙara dagula kasuwannin makamashi na duniya tare da haifar da ƙarin hauhawar farashin mai a kwanaki masu zuwa.

📌 Kaynak

Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
📱
News AI World — Mobil uygulama
Bu haberleri 45 dilde, anlık çeviriyle cebinde. Erken erişim için Gmail adresini bırak.
← Tüm haberlere dön