Me ya faru tsakanin maiɗakin El-Rufai da jami'an hukumar ICPC?
"Mu iyalansa muna cikin matsananciyar damuwa. Kullum muna rayuwa cikin fargabar mu wayi gari mu ji wani mummunan labari."
Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai sun koka game da yadda ake tafiyar da shari'arsa da ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya.
Kamar yadda maiɗakinsa Hajiya Asiya El-Rufai ta bayyana, "ana tauye haƙƙin mijin nasu da hana shi samun ƴancinsa" na ɗan'adam.
Ta ce ya kamata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar mijinta ya samu adalci kan yadda ake tafiyar da shari'arsa, domin acewarta El-Rufai bai cancanci hakan daga wajensa ba.
Hajiya Asiya ta yi waɗannan kalamai ne tare da matar El-Rufai ta biyu, Aichatou, a inda ta mayar da martani kan kama likitan da ke kula da lafiyar mijinta, Farfesa Bello Abubakar, abin da hukumar ta ICPC ta tabbatar a ranar Talata.
Da take ganawa da manema labarai a gidanta da ke Abuja, Hajiya Asiya ta ce iyalansu ba sa roƙon Shugaba Tinubu ya tsoma baki a shari'ar El-Rufai ko ya dakatar da gurfanar da shi a gaban kotu.
Sai dai ta ce abin da suke nema shi ne a tabbatar da tsohon gwamnan ya samu haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada ga kowane ɗan ƙasa, ciki har da samun kulawar likita, damar ganin 'yan uwansa da lauyoyinsa, da kuma beli bisa sharuɗɗan da suka dace.
Hajiya Asiya ta ce ta yi wa Tinubu kamfen a sassa daban-daban na jihar Kaduna domin ganin ya samu nasara zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma mijinta ma ya tsaya masa tsayin daka.
"Mai Girma Shugaban Ƙasa, na yi maka kamfen. Na zagaya lungu da saƙo na jihar Kaduna saboda kai. Mijina ya tsaya maka. Shin wannan ne abin da za a saka mana da shi?" in ji ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Ta ƙara da cewa, a ganinta, Shugaba Tinubu na da ikon tabbatar da an mutunta haƙƙoƙin mijinta.
"Kana iya dakatar da duk abin da ake yi idan ka furta kalma ɗaya. Mun yi imanin kai uba ne, kuma mun san za ka iya tausaya mana."
"Ba wai muna roƙon ka hana a gurfanar da shi ba ne. Muna so ne kawai a ba shi haƙƙoƙin ɗan'adam da kundin tsarin mulkin da ka rantse za ka kare ya tanada. A ba shi belin da zai iya cikawa. Idan yana da laifi, kotu ce za ta yanke hukunci, idan kuma ba shi da laifi, kotu ce za ta tabbatar da hakan."
Hajiya Asiya ta ƙara da cewa ci gaba da tsare El-Rufai tare da hana shi ganin likitocinsa da ƴan'uwansa ya jefa su cikin damuwa.
"Mu iyalansa muna cikin matsananciyar damuwa. Kullum muna rayuwa cikin fargabar mu wayi gari mu ji wani mummunan labari," in ji ta.
"A ganina, abin da ake yi ya fi kama da jefa damuwa ga Malam da kuma iyalansa domin an san abin yana taɓa tunaninmu. Suna ganin idan sun wulaƙanta mu, suka tauye mana mutunci, suka kuma sa mu cikin fargaba a ko
📌 Kaynak
Bu haber XML kaynağından derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →