Dalilin da ya sa Kim Jong Un bai taɓa magana game da mahaifiyarsa ba
‘Yan Koriya ta Arewa kaɗan ne suka san mahaifiyar Kim Jung Un, domin asalinta na iya jefa halascin mulkin ƙasar cikin haɗari.
Daga cikin ɗimbin asirai da suka lulluɓe shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, sirrin da ke tattare da mahaifiyarsa shi ne ya fi ɗaukar hankali.
A tsawon shekaru 15 da yake mulki, Kim bai taɓa ambaton sunanta a bainar jama'a ko sau ɗaya ba.
Saɓanin uwaye biyu da suka gabata a zuriyar su Kim Jong Un – Kang Pan Sok, mahaifiyar jagoran da ya kafa ƙasar, Kim Il Sung, da kuma Kim Jong Suk, mahaifiyar Kim Jong Il – wadanda aka daukaka a matsayin "iyayen Koriya", Ko Yong Hui kuwa mace ce da ba a fiya sanin ta ba, kuma babu wani abu da aka sanya masa sunanta.
Wannan tsauraran matakan na boye-boye game da Ko Yong Hui na iya samo asali ne daga abin da ake gani a matsayinta na zamantakewa mai rauni da kuma kasancewarta uwargida, abubuwan da masana ke cewa na iya zama barazana ga tsarin mulkin ƙasar.
Dangane da abin da masana tarihin rayuwa suka tattara, an haifi Ko a birnin Osaka, Japan a shekarar 1952. Mahaifanta sun ƴan asalin tsibirin Jeju a Koriya ta Kudu ta yanzu ne – wato yankin da ake ɗauka a matsayin na maƙiya.
A matsayin mazauna Japan, iyalan Ko sun kasance cikin rukunin "'yan Koriya na Zainichi" – wato baƙin haure da suka zauna a Japan tun lokacin mulkin mallakar Japan a yankin daga 1910 zuwa 1945.
Wadanda suka koma Koriya ta Arewa da farko ana kallon su da kishi domin sun koma da kudi, tufafi da kayan gida daga maƙwabciyar ƙasa mai tsarin jari-hujja.
Sai dai kuma an ba su laƙabin "jjaepo", kalma ta wulakanci da ake amfani da ita ga wata ƙungiya da ake ganin ta gurɓace da aƙidu na ƙasashen waje masu haɗari.
A cikin tsarin rarrabuwar zamantakewa mai tsauri na Koriya ta Arewa – wanda ake kira songbun – 'yan Koriya na Zainichi suna cikin "aji mai rauni", bisa dogaro da tsari aji-aji a cikin al'umma.
Ana sanya musu ido sosai daga gwamnati, kuma da mafi yawancin lokuta ana hana su shiga jami'o'i masu inganci ko kuma samun ayyuka masu kyau da makoma.
Al'ummar Koriya ta Arewa na da tsari mai tsananin bambancin matsayi, wanda wasu masana ke cewa yana kama da tsarin "caste" da ke bambance ƙimar mutum ta hanyar asalinsa.
Haka kuma wani "tsari ne da ake hukunta mutum bisa abin da wani dan uwansa ya aikata", inda ake ladabtar da 'yan ƙasa saboda ayyukan 'yan uwansu, a cewar Dakta Jeung Young-tae na Jami'ar Dongyang.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Lokacin da take kusan shekara 10 da haihuwa, iyalan Ko sun yi hijira zuwa Koriya ta Arewa.
Iyalan nata suna cikin kimanin mutane 93,000 na Koriya da suka koma ƙasar kwaminisanci daga Japan tsakanin 1959 da 1984 ƙarƙashin shirin "Aljannar Duniya" – wani tsari da ya yi alkawarin ra
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →