''Ba a yi adalci in aka ce matsalar tsaro ta taɓarɓare a mulkin Tinubu ba''

📰 Gündem 📰 BBC Hausa 🕐 10 saat önce
''Ba a yi adalci in aka ce matsalar tsaro ta taɓarɓare a mulkin Tinubu ba''

A cewar wani mai magana da yawun shugaba Tinubu, duk da cewa da gaske ana samun garkuwa da mutane, to amma lamarin bai kai yadda aka gani kafin hawansa karagar mulki a shekarar 2023 ba.

Yayin da 'yan Najeriya da dama ke ci gaba da kokawa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar a shekaru uku na farko na mulkin shugaba Tinubu, fadar shugaban kasar ta dage cewa lallai ana samun nasara a kokarin yaki da matsalar.

A cewar wani mai magana da yawun shugaba Tinubu Abdulaziz Abdulaziz, duk da cewa da gaske ana samun garkuwa da mutane, to amma lamarin bai kai yadda aka gani kafin hawansa karagar mulki a shekarar 2023 ba.

A cewarsa ''Bana jin an yi adalci idan aka ce matsalar tsaro na tabarbarewa a mulkin Tinubu, watakila dai a ce tana kara fadada, mun sani ba ma jin dadi, kuma ba wai muna watsi da halin da wadanda suke cikin matsalar suke bane, gwamnati ba ta jin dadi, amma idan ka duba abun da aka saba samu a baya, tsananin abun, ka ji an ce an shiga gari daya an sace mutum dari biyu, an je nan gari an kashe mutum 50 lokaci daya, ko ka ji an an tashi gari an watsa shi, yanzu ana samun irin haka jifa-jifa, amma ba irin manyan hare haren da za ka ji an ce an sace ko an kashe mutane da yawa kamar yadda take faruwa a baya ba''.

Ya ce hatta satar mutanen da ake samu a yanzu sai dai a sace kalilan amma ba wai da yawa kamar yadda ake samu a baya ba.

''A yanzu sai dai ka ji an saci yara 26, nan an saci yara 42, ba shakka ko mutum daya aka sace abu ne na takaici, amma ka tuna an saci yara 300 a baya an shiga da su daji, an dauki mutane dari biyu da wani abu a jirgin kasa wata da watanni ba a iya gano su ba, amma a wannan gwamnatin ba yadda za ka ji an ce an sace yara ba a yi kokari cikin kankanin lokaci an ceto su ba'' inji shi.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce duk da ƙoƙarin jami'an tsaro, har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai domin dawo da cikakken zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

A gefe guda kuma, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa tattalin arziƙin Nijeriya na nuna alamun farfaɗowa a hankali sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin ta aiwatar tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023.

A cewar gwamnati, matakan da aka ɗauka sun taimaka wajen ceto ƙasar daga matsananciyar matsalar tattalin arziƙi da ka iya jefa ta cikin durƙushewa, duk da cewa miliyoyin 'yan Najeriya sun fuskanci tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi a cikin shekaru ukun da suka gabata.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Shi dai shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya cika shekara uku a kan mulki a ƙarshen watan Mayu, ya fara mulkinsa da wasu manyan sauye-sauye da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma sassauta tsarin canjin kuɗi ta yadda darajar naira za ta rinƙa ƙayyadewa bisa ga yanayin

#war

📌 Kaynak

Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
← Tüm haberlere dön