Alamu na nuna Kim Jong Un na shirya ƴarsa domin ta gaje shi

📰 Gündem 📰 BBC Hausa 🕐 1 gün önce
Alamu na nuna Kim Jong Un na shirya ƴarsa domin ta gaje shi

Yarinyar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na cigaba da jan hankali, musamman ganin yadda take gudanar da rayuwar ƙasaita. Sai dai irin shigar da take yi da irin rayuwar da take yi, sai ake kallon Kim Ju Ae ta fara kama hanyar zama wadda za ta maye gurbin shugaban mai cikakken iko.

Yarinyar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na cigaba da jan hankali, musamman ganin yadda take gudanar da rayuwar ƙasaita.

Sai dai yadda ake mata kallon yarinya matashiya, irin shigar da take yi da irin rayuwar da take yi, sai ake kallon Kim Ju Ae ta fara kama hanyar zama wadda za ta maye gurbin shugaban mai cikakken iko.

Rahotanni na cewa an haife ta ne a shekarar 2013, amma an fara jin ɗuriyarta ne a lokacin da ta kai shekara 9.

A watan Nuwamban 2022 ne aka fara ganinta tare da mahaifinta suna rangadin wasu makamai masu linzami.

Tun daga lokacin ne ta fara jan hankali a ƙasar, duk da yanzu ta ƙara faɗaɗa yadda take shiga ta nuna isa da ƙasaita.

A 2020, Koriya ta Arewa ta ɗabbaƙa dokar da ta kira "Reactionary Ideology and Culture Rejection Act" domin hanawa ko taƙaita shiga da amfani da al'adun turawan ko ƙasashen waje.

Amma a shekarar 2023, kafar talabijin ɗin ƙasar ta fitar da wani bidiyo na Ju Ae tare da mahaifinta sanye da farar rigar sanyi da aka ruwaito cewa farashinta ya kai dala 1,900 da aka sayo daga kamfanin sayar da kayan ado na Christian Diro na Faransa.

Bayan shekara ɗaya kuma, sai aka ga Ju Ae sanye da wata babbar bulawus a wani babban taro da aka yi a babban birnin ƙasar, Pyongyang.

Daga bisani an saki wani faifan bidiyo inda aka ciki aka soki yanayin shigarta, tare da gargaɗin cewa gashinta ya saɓa da al'adun ƙasar.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Amma a yanzu wasu sun fara kwaiwakyon salon shigar Ju Ae ta ƙasaita a sassan ƙasar.

"Yanzu zamani na canja, komai na canja cikin sauri," in ji Joung Eunlee, shugaban sashen bincike a cibiyar haɗin kan Koriya ta Arewa.

"Tun daga shekarar 2010, adadin masu zuwa ƙasashen waje suna aiki suna samun kuɗaɗen ƙasashen waje sun ƙaru sosai."

Kusan ƴan Koriya ta Arewa 2,000 ne suka kasance a China a lokacin annobar Covid-19, sannan lokacin da "suka koma birnin Pyongyang... sai suka koma da al'adun da suka koya a can."

"A shekarun baya, kayayyakin ado na ƙasaita na zuwa ne kawai daga kamfanin Zainichi na Japan. Amma yanzu alamu na nuna cewa ƴan Koriya ta Arewa sun fara sabawa da kayayyakin ƙasashen waje."

"Kasancewar jakukkuna da takalma suna da tsada (saboda fasaƙaurinsu ake yi zuwa ƙasar) sai ya zama an fi cin kasuwar turare a ƙasar a yanzu."

Amma dai ba Ju Ae ba ca ta fara fice da ado da shiga ta ƙasaita a zuriyarsu.

"Alamu na nuna cewa Ju na shiga ne da salo irin na mahaifiyarta Ri Sol Ju," in ji mataimakin daraktan cibiyar Sejong, Cheong Seong-chang.

"Ta hanyar amfani da shiga irin ta ƙasashen turai, Ju Ae da Ri Sol Ju na zama na daban, inda suka bay

#war

📌 Kaynak

Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.

Orijinal haberi oku →
← Tüm haberlere dön