Ƙasashen da suka taimaka wa Najeriya da waɗanda suka goyi bayan Biyafara a yaƙin basasa
Wasu ƙasashen Afirka da Turai da ma sauran sassan duniya sun tsoma kansu ciki ta hanyar karkata wani ɓangare, musamman ta hanyar bayar da agajin kayan soji ko tallafi ko kuma diflomasiyya.
Yaƙin basasar Najeriya na Biyafara da ya gudana daga shekarar 1967 zuwa 1970 bai taƙaita ga Najeriya kawai ba, sai dai yaƙi ne da ya ƙunshi sanya hannu da bakin ƙasashen duniya, lamarin da ya yi matuƙar tasiri a yaƙin.
Wasu ƙasashen Afirka da Turai da ma sauran sassan duniya sun tsoma kansu ciki ta hanyar karkata wani ɓangare, musamman ta hanyar bayar da agajin kayan soji ko tallafi ko kuma diflomasiyya.
Ga jerin wasu daga cikin ƙasashen da suka yi tasiri a yaƙin:
A farkon yaƙin Biyafara, Ghana ce ƙasa ta farko da ta gabatar da kanta a matsayin mai shiga tsakani domin kawo sulhu.
A watan Janairun 1967, shugaban ƙasar Ghana Janar Jeph Ankrah ya shirya wani taron zaman sulhu, inda jagororin ɓangarorin biyu da ke adawa da juna - Shugaban Najeriya Yakubu Gowon da jagoran Biyafara Chukwuemeka Ojukwu - suka zauna gaba da gaba a teburin tattaunawa domin ganin yadda za a warware rikicin.
Da farko an cimma yarjejeniya a lokacin, wadda aka yi wa laƙabi da 'Aburi Agreement', to amma rashin kyakkyawar fahimta da kuma rawar da kowane ɓangare zai taka sai ya ƙara ƙazanta yaƙin.
Yayin da yaƙin ya ɓarke, kawunan ƙasashen duniya sun rarrabu, wasu sun goyi bayan Najeriya, wasu kuma sun goyi bayan Biyafara.
Tarayyar Soviet ta goyi bayan Najeriya ne, inda ta riƙa taimaka wa sojojin Najeriya da makamai.
Jaridar New Yor Times ta Amurka ta ce tun daga farkon yaƙin, Tarayyar Soviet ta riƙa tallafa wa Najeriya a siyasance da kuma ta fannin soji, duk da cewa babu wata kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu gabanin ɓarkewar yaƙin.
Rahoton jaridar ya ce Soviet ta tallafa wa Najeriya da jiragen yaƙi da makaman atilare da kuma jiragen ruwan sintiri, wanda hakan ya taimaka wa Najeriya sosai a yaƙin.
A nata ɓangaren, Birtaniya wadda ita ce ta yi wa Najeriya mulkin mallaka ba ta goyi bayan ɓallewar Najeriya ba.
A dalilin haka ne ta samar wa Najeriya tallafi, ta bayar da kariya ga kamfanin haƙar man fetur na Shell tare da tallafa wa Najeriya a alƙarta da ƙasashen ƙetare.
Bayanai sun ce tallafin da Amurka ta bai wa gwamnatin Najeriya ya samo asali daga muradinta na ganin ta tabbatar da ci gaba da wanzuwar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya.
Masar ta tallafa wa Najeriya ne da dabaru da kayan yaƙi ta sama, ta hanyar tura wa Najeriya jiragen yaƙi.
Shugaban Masar na wancan lokaci Gamal Abdel Naseer ya taka rawa, ta hanyar ganin Najeriya ta samu jiragen yaƙi, musamman na Soviet, da matuaƙa da kuma masu gyaran irin waɗannan jirage.
Amurka na daga cikin ƙasashen duniya da ake ganin sun yi ta yunƙurin tsayawa tsakiya a lokacin rikicin na Biyafara.
Hakan ya sanya rawar da Amurka da kum
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →