Ko ana kama ƴan bindiga masu neman kuɗin fansa ta waya a Najeriya?
Ko a baya-bayan nan wasu ƴan bindiga sun sace wani tsohon babban jami'in sojan Najeriya, kuma rahotannin kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun bayyana cewa waɗanda suka sace shi sun gabatar da buƙatunsu ta hanyar wayar tarho.
Najeriya na fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, wanda ya haɗa da rikicin Boko Haram da na ƴan bindiga masu kisa da kuma satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Ko a baya-bayan nan wasu ƴan bindiga sun sace wani tsohon babban jami'in sojan Najeriya, kuma rahotannin kafofin yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa waɗanda suka sace shi sun gabatar da buƙatunsu ta hanyar wayar tarho.
Sai dai wani abu da ya daɗe yana rikitar da al'umma shi ne yadda irin wadannan ƴan bindiga ke shafe watanni suna waya da ƴan'uwan waɗanda suka sace domin sasantawa kan kudin fansa da za a biya.
Haka nan wani abu da ya yawaita a baya-bayan nan shi ne yadda wasu da ake zargin ƴan fashin daji ne ke yin bidiyonsu a daji suna yaɗawa a shafukan sada zumunta na tiktok, ko ma "bayyana kai-tsaye a bidiyoyi na tiktok" domin kare kansu.
"Babu shakka ƴan bindiga na amfani da yanar gizo wajen nuna bajinta da ayyukan da suke yi," in ji masanin tsaro a yankin Sahel kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting, Kabiru Adamu.
Amma me ya sa ba a yawan jin labarin cewa an kama irin wadannan ƴan bidiga masu magana da ƴan'uwan wadanda suka sace ko kuma suke bayyana a bidiyoyin tiktok?
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Tukur Burutai na cewa "ƙasar na da ƙwarewar da za ta iya bibiyar ƴan bindiga".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
"A wannan zamani yanar gizo da kafafaen sada zumunta kafafe ne na tattara bayanai (intelligence) a bayyane (OSINT) ko kuma 'Open Source Intelligence', kuma ya kamata a ce kowane ɓangare tsaro na amfani da shi".
Masanin ya bayyana cewa ƙasashen duniya da dama kamar Amurka da sauran ƙasashen Turai, sun riga sun fitar da tsarin tattara bayanai ta wannan fage na intanet.
Sai dai ya ce a ƙasashe irin su Najeriya akwai rashin yarda daga hukumomin yaƙi da tsaro wajen amfani da tsarin duk da cewa duniya ta rungume shi.
Amma ya ce a baya-bayan nan Najeriya ta fara ɗaukar matakan bin wannan tsari "sai dai ba su fara amfani da shi tare da saka shi cikin tsarin yadda ya kamata ba".
Ya bayyana cewa a misali, "akwai ƙarancin bayani kan ko an taɓa amfani da wannan tsarin tattara bayanai wajen kama masu laifi, amma kuma akwai shaidun da ke nuna cewa an yi amfani da bayanan yanar gizo wajen kama mutane da suka bayyana ra'ayoyin da suka saɓa wa hukumomi."
Ɓangare mai muhimmanci, ko kuma a ce mataki na farko wajen amfani da wannan tsari na kama masu laifi ta hanyar fasahar sadarwa shi ne tattara bayanai.
Kabiru Adamu ya ce "babu shakka gwamnati na da na'urori na bibiyar bayanai
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →