Peter Obi ya buƙaci ƴanbindiga su saki ɗaliban da suka sace
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 03/06/2026.
Shugaban Hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ya ragu sosai sakamakon ci gaba da yin gwaje-gwaje.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce a yanzu mutanen da suke ɗauke da cutar ba su wuce 116 ba, daga dubu ɗaya da ake da su a makon da ya gabata.
Ya kuma ce gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da mutum 340 ne suka kamu da cutar a Jamhuriyar ɗimokraɗiyyar Kongo, ciki har da mutum 60 da suka mutu.
Tedros ya ce ya samu ƙarfin gwiwa na irin ƙoƙarin da ake yi na daƙile ɓarkewar cutar a yayin ziyarar da ya kai a baya bayan nan.
Sai dai ya ce har yanzu akwai ƙalubale ciki har da yin gwaji da kuma bibiyar waɗanda suka yi alaƙa da masu ɗauke da cutar.
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →