Me ya sa Isra'ila da Hezbollah ke son kame ganuwa mai shekara 900?
Wani hoton bidiyo da sojojin Isra'ila suka saki ya nuna wasu dakarun sojin ƙasar na ratsawa ta cikin wata tsohuwar ganuwa da ke kan tsauni wadda aka gina tun zamanin da
Wani hoton bidiyo da sojojin Isra'ila suka saki ya nuna wasu dakarun sojin ƙasar na ratsawa ta cikin wata tsohuwar ganuwa da ke kan tsauni wadda aka gina tun zamanin da, kafin daga bisani dakarun su kafa tutar Isra'ila. Isra'ila ta yi iƙrarin kame gidan sarautar Beaufort Castle da ke kudancin Lebanon, a karo na biyu.
"A ranar Lahadi, bayan kame ganuwar, firaiministan Isra'ila ya kira hakan da 'wani mataki mai muhimmanci da kuma babban sauyi a manufofinmu.'"
"Mun cire tsoro," in ji Benjamin Netanyahu. "Muna ɗaukar matakin jagoranci. Muna aiki a dukkan ɓangarori — a Siriya, a Gaza, a Lebanon."
"Hakan na zuwa ne yayin da dakarun Isra'ila ke ƙara kutsawa cikin yankin Lebanon, har sun ƙetare iyakarsu ta farko da aka kafa a kogin Litani."
"Birtaniya da Faransa da Jamus sun soki sabbin hare-haren Isra'ila a kan Lebanon, yayin da rundunar sojin Isra'ilar (IDF) ta gargadi karin mazauna su fice daga wani babban yanki na kudancin Lebanon. Firaiministan ƙasar Leabon ya zargi Isra'ila da aikata 'hukunci na kan mai uwa da wabi'."
Wannan ba shi ne karo na farko da Isra'ila ta yi iko da ganuwar Beaufort ba. Rundunar sojin Isra'ila ta ƙwace ganuwar shekaru 44 da suka gabata, a lokacin abin da Isra'ilawa ke kira Yaƙin Lebanon na Farko. Don fahimtar dalilin da ya sa ake gwabza yaƙi mai tsanani kan wannan wuri, ya dace a duba tarihin ganuwar da kuma muhimmancinta da na tsaunin da take kansa, ta fuskar dabarun soja.
Wasu masana tarihi na ganin cewa an fara yi wa tudun garkuwa ta hanyar gina takanga tun a zamanin Romawa — amma ganuwar yadda take a yau ta samo asali ne daga ƙarni na 12.
A zamanin Yaƙin da mabiya addinin Kirista suka ƙaddamar — tsakanin ƙarshen ƙarni na 11 zuwa na 13 — an ga rundunonin Turai suna gina jerin ganuwa a saman tuddai a yankin Levant, domin kare hanyoyin da ke tsakanin bakin teku da garuruwa na cikin ƙasa. Ganuwar Beaufort ta zama ɗaya daga cikin mafi muhimmanci. A shekara ta 1190, Salahuddeen, jagoran Musulmi da ya yaƙi mayaƙan Kirista kuma ya sake fasalin yankin, shi ne ya ƙwace ganuwar.
Majiyoyin turai sun ce ganuwar ta samo sunanta ne na "Beaufort" ne daga harshen Faransanci da ke nuni da yadda aka aka gina ganuwar a kan tudu. Sunanta na Larabci shi ne Qal'at al-Shaqif ko kuma Shaqif Arnoun da ke nufin ganuwa a kan tsauni.
Tarihinta na da alaƙa da irin yadda aka gina ta wanda ya zama na daban, kasancewar ta haɗa tsarin gini da mayaƙan Kirista da ake kira Crusader da kuma tsarin gini na Musulman gabashi. Kuma tun a shekarar 2024, ganuwar ta Beaufort ta shiga jerin wuraren tarihi da ke ƙarƙashin kariyar yarjejeniyar Hague wadda ta hana a t
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →