Nau'in ciwon suga da ke kama siraran mutane
An gano cewa ciwon suga nau'in Type 5 na faruwa ne sanadiyyar tsawon lokaci ba tare da samun abinci mai gina jiki ba, musamman idan mutum ba ya samun ingantaccen abinci na tsawon lokaci ko kuma a lokacin girma. Sai dai har yanzu masana ba su kammala amincewa ko da gaske ciwon na wanzuwa ba ko a'a'.
Lokacin da suka fara yi wa Noella Mukumbi allurar sinadarin insulin, sun yi amanna cewa suna kokarin ceton rayuwarta ne. Amma a madadin haka, yar asalin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo mai shekara 30 ta ce maganin ya sa ta rika ji kamar za ta mutu.
An gano cewa Noella, wadda ke aikin gyaran gashi, tana da ciwon suga nau'in 1 a shekarar 2023, amma ta ce tana jin cewa akwai wani abu da ba daidai ba ne.
Bayan fara yi mata allurar insulin da ake yi kullum, matar mai 'ya'ya biyu ta ce ta rika jin jiri kuma ba ta da kuzari. Kwatsam, wata rana sai ta faɗi.
Ta shaida wa BBC cewa "Ina tsakar shirya tufafin yara sai kawai mijina ya same ni a ƙasa ina ihu,"
Byan shekara uku, sai kwararrun likitoci suka fada mata cewa wataƙila tana da ciwon suga na nau'in 5 ne.
Ciwon suga, wanda alkalumma ke cewa akwai mutane sama da miliyan 830 da ke fama da shi a faɗin duniya, yana faruwa ne idan wasu sinadaran jikin mutum suka shafi yadda jiki ke tantance yawan sukarin da aka sanyo da ke cikin jikin mutum, abin da ke nuni da cewa akwai hatsari.
Nau'in 5 wani nau'i ne na cutar da ake kyautata zaton yana samuwa bayan rashin abinci mai gina jiki na tsawon lokaci, musamman a lokacin ƙuruciya ko tsakanin matasa. A bara Hukumar Kula da Ciwon Suga ta Duniya (IDF) wadda ke wakiltar ƙungiyoyin masu ciwon suga 251 na ƙasa, ta amince da shi a hukumance, .
Sai dai duk da haka, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta amince da wannan cuta ba, wadda ta yi amanna cewa har yanzu babu isassun hujjoji da za su nuna cewa wata nau'in cutar ce daban ba irin sauran ba.
Wasu masana kimiyya sun yarda cewa akwai mutane akalla miliyan 25 nau'in 5, kuma sun yi gargadin cewa idan har kuskure wajen gwaji aka dauka daidai ta ke da sauran nau'ikan cutar, to lallai za a samu ahasar rai?
Dr Meredith Hawkins, daraktan Cibiyar Kula da Ciwon Suga ta Duniya a Kwalejin Magunguna ta Albert Einstein, ta ce rashin tantance rarrabawar ciwon suga domin ware kowanne nau'i "matsala ce da ta yawaita" wadda ke haifar da mace-mace sakamakon rashin amfani da maganin insulin yadda ya kamata.
"Yawancin waɗannan matasan da muka yi jinya, mutuwa suka yi.'' in ji ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Ciwon suga na nau'in 1 yanayi ne na garkuwar jiki wanda jiki ke daina samar da insulin, yayin da ciwon suga na nau'in 2 yana da alaƙa da sauyi a juriyar insulin.
Amma masana kimiyya sun ce nau'in 5 zai iya kasancewa mai alaƙa da rashin abinci mai gina jiki na yau da kullun, wanda ke shafar ci gaban pancreas, sashin da ke samar da insulin.
Zai yi wu masu cutar su iya samar da insulin, amma ba ya is
📌 Kaynak
Bu özet BBC Hausa kaynağından otomatik derlenmiştir. Tamamı için orijinal habere gidin.
Orijinal haberi oku →